Isra'ila ta bude sabon babin sulhuntawa da ƙasashen Larabawa

  • Daga Frank Gardner
  • Wakilin BBC kan Tsaro
Israeli and United Arab Emirates flags line a road in the Israeli coastal city of Netanya, on August 16, 2020

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Israeli and UAE flags lined this road in the Israeli coastal city of Netanya

''An kafa tarihi,'' ''Ban mamaki''; ''Wani abu da zai kawo sauyi''; ''Cin amana'': babu wata kalma da za ta yi karanci wajen bayyana sanarwar da aka yi a watan nan ta ba-zata - daga bakin Shugaba Trump - cewa Kasar Hadaddiyar Daular Larabawa da Isra'ila sun cimma yarjejeniyar ƙawance irin na Diflomasiyya.

Tun bayan yarjejeniyar zaman lafiya da Masar ta kulla da Isra'ila a shekarar 1979, da kuma ta Jordan da ta biyo baya a 1994, lamarin na baya-bayan nan ya sa kasar UAE ta zamo ta uku a kasashen Larabawa da ta kulla alaka da Isra'ila.

Ita ce kasa ta farko cikin kasashen Larabawa masu arziki na yankin Gulf guda shida da ta fara daukar wannan matakin. Ana sa rana Oman da Bahrain da watakila Moroko za su bi sahunta a nan kusa.

An yi ta boye tuntubar juna da aka yi ta yi tsakanin UAE da Isra'ila tsawon shekaru, ta yadda aka ƙi bayar da kofar sanin me ke faruwa kan wannan yarjejeniya har sai da aka zo matakin karshe.

Babu wata tuntuba tsakanin ma'aikatar harkokin wajen UAE da na makwabtanta Larabwa. Kusan an shammaci kowa, musamman ma Falasdinawa, wadanda suka kira lamarin ''tamkar an caka musu wuka ne a gadon baya'' tun da har yanzu ba su ko kai kusa ga samun kasarsu ta kansu ba ko kuma kawo karshen mamayar Isra'ila.

''Ga Falasdinawa, babu wani cigaba anan,'' kalaman Emile Hokayem na cibiyar nazarin tsare-tsare da ke Landan kenan.

Ga yarima Sheikh Mohammed Bin Zayed (Wanda ake kira da MBZ), wannan yarjejeniya ce da ake iya kwatantawa da wata caca sai dai wannan akwai wanda ake son farantawa.

Barazanar ita ce hakan zai rage farin jinin shugabancin UAE a kasashen Larabawa inda tuni wasu sakonnin kafofin sada zumunta ke ambatar ''a sayar da ita''.

Idan shugaban Isra'ila Benjamin Netanyahu ya cika alkawarinsa na janyewa daga wani bangare na Gaɓar Yamma da Kogin Jordan to hakan zai kasance abin kungiya ga Emirates da kuma tabbatar da zargin da ake yi kan yarjejeniyar.

Bayanan bidiyo, Israel annexation: What is the West Bank?

Sai dai wannan yunkuri na iya samun cikas daga fadar White House, sannan zanga-zanga a tittunan kasashen Gulf ba abu ne da ke samun amincewa ba.

Mene ne ke cikin wannan yarjejeniya, kuma me hakan ke nufi ga wannan yanki na Gulf wanda a baya ke samun kariya daga Burtaniya kafin ƙasar ta zama mai cin gashin kanta a 1971?

A takaice, abu biyu ne - dabarun tsare-tsare da fasaha.

Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa tare da Bahrain da Saudiya, akwai rashin yarda tsakaninsu, da fargaba, ga barazanar maƙwabciyar ƙasar ta ruwa da ke da karfin soji: Iran.

A Palestinian protester stands on a photo of Abu Dhabi Crown Prince Mohammed bin Zayed at a protest in Bethlehem against the UAE's decision to normalise relations with Israel (16 August 2020)

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Falasdinu ta soki matakin da Hadaddiyar Daular Larabawa ta dauka na yaukaka dangantaka da Isra'ila

Shugabanin Larabawar yankin Gulf sun dubi taswirar yankin da adana bayanai kan yadda duk da durkushewarta saboda takunkumi, matsayin Iran da dabarunta ya yadu a gabas ta tsakiya tun lokacin aka cire kariyar da gwamnatin Saddan Hussein ta yi a Iraqi.

Duk da cewa an dakatar da karfin Iran zuwa iyakokinta, a yau karfin mayakanta na fitowa a Iraqi da Syria da Lebanon da Yemen. Isra'ila ta nuna damuwarta, musamman kan shirin nukiliyar Iran.

A zahiri, wannan shi ya assasa hadin-kai amma ba a hukumance ba tsakanin shugabanin kasashen gabas ta tsakiya masu tsatsauran ra'ayi, tawagar da ake yiwa kallon masu ra'ayin mulkin kama karya, Isra'ila ta amsa cewa ita ma tana cikin mambobin wannan kungiya.

UAE na da lalitar arziki mai girma - ta na da tarin arzikin mai da take ajiya da ma'aunin tattalin arzikin kusan $40,000 (£30,000). Kasar ta kasance mai buri a duniya, ita ce kasar larabawa ta farko da ke aike sako duniya Mars.

Bayanan bidiyo, Jared Kushner: "Wannan babbar dama ce da za ta kawo sauyi a Gabas Ta Tsakiya"

Isra'ila tana kan gaba sosai a fanin fasaha a gabas ta tsakiya, inda take yawan kirkire-kirkire. Kuma idan wannan alaka tasu ta yi nasara, to za ta yi tasiri wajen sake haɓɓaka UAE don shiga sabon babin ci gaba da samun matsayi a duniya, gami da samar da ayyukan yi ga 'yan kasar da ke tasowa.

Alakar Isra'ila da yankin Gulf a shekarun baya.

A 1995, fira ministan Isra'ila Yitzhak Rabin da Yahudawa suka hallaka, ya aika ministan harkokin waje Shimon Peres zuwa wata ziyarar aiki ƙasashen Oman da Qatar.

An bude wani ofishin cinikayya tsakanin kasashen biyu a biranensu. Na tuna lokacin da na kira ofishinsu a Muscat domin tsokaci - wakilin Isra'ila na amsa kiran waya da gaisuwa ta harshen Hebrew ''Shalom'' kafin daga bisani ya yi sauri ya sauya zuwa harshen Larabci ''Salaamu aleikum''.

Shirin kasuwancin ya ja da baya bayan Mista Netanyahu ya zama fira minista, Isra'ila ta shiga tsakani a Lebanon lokacin rikicin intifada na Falasdinawa ya sake bazuwa.

A baya-bayan nan alakar diflomasiya ta sirri tsakanin Isra'ila da kasashen Gulf na sake ruruwa yayin da ake sake nuna fargaba a kan kasar Iran.

Kasahen Bahrain da Oman da Qatar na iya bin sahun Haɗaɗɗiyar Daular Larabwa su cimma tasu matsayar.

Oman's Minister of State for Foreign Affairs, Yusuf bin Alawi bin Abdullah (L), shakes hands with Israeli Prime Minister Benjamin Netanyahu (R) prior to a meeting in Warsaw, Poland on 13 February 2019

Asalin hoton, Anadolu Agency

Bayanan hoto, Oman ba ta da huldar hjakadanci da Isra'ila, sai dai manyam jami'an kasashen suna hulda da juna

Saudi Arabia na iya daukan tsawon lokaci. Amma a 2002 lokacin da Yarima Abdullah ya sanar da shirin yarjejeniyar zaman lafiya a taron kasashen larabawa a Beirut, ya yiwa Isra'ila tayin aminta da kasar idan ta amince da sharudansu kan iyakoki na 1967.

Yarjejeniyar ta jefa Friministan Ariel Sharon cikin dogon nazari kafin daga baya cikin kwanaki Hamas ta kaddamar da harin bama-bamai hakan ya rusa tattaunawar. Yau gabas ta tsakiya ta kasance wata sabuwar duniya da baa taba tunanin zata shiga wannan yanayi a zahiri ba.